Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun ce kimanin mutane 150,000 ne suka tsere daga kudancin birnin Khan Yunus da ke zirin Gaza tun daga ranar litinin, a daidai lokacin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da kai munanan hare-hare a yankin da aka yi wa kawanya.
Louise Wateridge, daga Hukumar Ba da Agaji da Ayyuka ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA, ya bayyana a yau Laraba cewa Falasdinawa sun tsere daga birnin bayan da Isra’ila ta ba da sanarwar cewa su fice daga birnin.
“Sama da kashi 80% na zirin Gaza na karkashin umarnin ficewar dukkanin ko kuma sojojin Isra’ila sun sanya su a matsayin wuraren yaki ,” in ji Wateridge.
Jami’in na Majalisar Dinkin Duniya ya ci gaba da cewa mutane na kaura zuwa Dayr al-Balah da kuma yammacin Khan Yunis, wadanda tuni ke da cunkoson jama’a.
“Suna da matsuguni mai kunci . Da kyar za su iya karbar Karin mutane a wadannan wuraren,” in ji Wateridge.
A waje guda kuma, ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya OCHA ya bayyana cewa, ta hanyar sanya ido kan yadda jama’a ke tafiya a kasa, ya kiyasta cewa mutane 150,000 ne suka tsere daga Khan Yunis.
Hukumar ta ce mutane da yawa “sun makale a wurin da tuni aka kwashe mazauna cikinsu, ta yadda ta wuya a iya yin wani abu na tallafa musu.