Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Ce: Har Yanzu Batun Gaza Shi Ne Batu Mafi Fifiko A Duniyar Musulmi

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Har yanzu batun Gaza shi ne batu mafi fifiko a duniyar Musulmi Jagoran juyin juya halin Musulunci

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Har yanzu batun Gaza shi ne batu mafi fifiko a duniyar Musulmi

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada wajabcin yin kyakkyawar mu’amala mai ma’ana tsakanin Majalisar Shura ta Musulunci ta Iran da sabuwar gwamnatin kasar, yana mai bayyana cewa nasarar da shugaban kasar da sabuwar gwamnati suka samu nasara ce ga kowa da kowa.

Shafin sadarwa na yanar gizo na Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya habarta cewa: Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada a yayin ganawarsa da shugaban kasar da ‘yan Majalisar Shura cewa: Wajibi ne su yi imani a cikin zukatansu cewa; Nasarar da zababben shugaban kasar zai samu wajen tafiyar da kasar, nasara ce ga kowa da kowa.

Jagoran ya yi imanin cewa kowa da kowa zai taimaki zababben shugaban kasa wajen gudanar da ayyukansa ga al’umma, domin nasarar da zai samu wajen gudanar da ayyukansa da tafiyar da kasa da bunkasa harkar tattalin arziki da al’amuran kasa da kasa da kuma al’adu, nasara ce ga kowa da kowa. Yana mai jaddada cewa dole ne Imani da hakan a cikin zukata.

Jagoran juyin juya halin na Musuluncin ya kara da cewa: Wajibi ne kowa da kowa ya ji cewa akwai hadi kai da fahimtar juna wajen gudanar da aiki tsakanin gwamnati da majalisar shura ta Musulunci kan muhimman batutuwa domin tabbatar da zaman lafiyar kasa da samar da hadin kai a tsakanin al’umma da yanke fata da burin makiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments