Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Falasdinawa

Ana ci gaba da samun shahadar Falasdinawa sakamakon hare-haren wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya kan Zirin Gaza Yayin da hare-haren wuce gona da iri

Ana ci gaba da samun shahadar Falasdinawa sakamakon hare-haren wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya kan Zirin Gaza

Yayin da hare-haren wuce gona da iri kan Gaza ya cika kwanaki 288, sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kashe-kashen gilla da kuma hare-haren wuce gona da iri, musamman kai hare-hare kan sansanonin da aka tsugunar da ‘yan gudun hijira da suka rasa muhallansu, a lokaci guda kuma sojojin sahayoniyyan suna kara tsaurara matakan killace yankin tare da kashe mazaunansa ta hanyar amfani da yunwa da hana shigar da kayan agaji, toshe hanyoyin shigar ruwa da kuma hana fitar da marasa lafiya daga yankin domin neman magani.

Rahotonni sun bayyana cewa: Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren wuce gona da irin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila kan Gaza ya karu zuwa shahidai 38,884 da kuma jikkatan wasu 89,459 tun bayan da suka fara kai hare-hare kan yankin a ranar 7 ga watan Oktoban bara, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta tabbatar da hakan.

A halin da ake ciki yanzu haka, majiyoyin lafiya sun ce Falasdinawa 8 ne suka yi shahada, yayin da wasu kuma suka jikkata a wani hari da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan wani gida a sabon sansanin da ke Nuseirat a tsakiyar Zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments