Hukumar Agaji ta Falasdinawa ( Unruwa) ta bayyana cewa;mutanen Gaza sun rasa duk wani abu wanda yake karfafa rayuwa, tare da yin kira da a bude dukkanin mashigan kai kayan abinci zuwa yankin.
Hukumar ta kara da cewa; Mutanen Gaza suna da bukatuwa da kowane abu, domin suna rayuwa ne a cikin yanayi mai wahalar gaske, maganin haka kuwa kadai shi ne shigar da Karin kayan abinci cikin yankin.
Hukumar ta wallafa wani bayani a shafin X dake cewa: Shata ta taru ta yi dandazo, kuma da akwai karancin gidajen wanka a zirin Gaza, ga shi kuwa an shiga lokacin zafi mai tsanani, lamarin da zai sa harkokin lafiya su kara tabarbarewa.”
Tun a baya dai shugaban hukumar Agajin ta Falasdinawa Phillip Lazarani ya bayyana da ake ciki a Gaza da cewa; Da akwai yanke kauna akan lamarin, haka nan kuma ya yi kira da wajabcin fuskantar yunwar da ake fama da ita a yanki.”
Sojojin HKI suna cigaba da kai hare-hare a cikin wannan yankin da y zuwa yanzu ya yi sanadin shahadar dubban mutane da kuma jikkata wasu dubban da lalata gidaje da gine-ginen muhimman cibiyoyi.