Yemen: Sojojin Yemen Sun Kai Hari Akan Wani Jirgin Ruwan Kasuwanci Na Birtaniya

Hukumar da take kula da harkokin kasuwanci a kasar Birtaniya ta sanar da cewa; jirgin kasar na kasuwanci ya nutse a cikin ruwan tekun “Red-Sea”.

Hukumar da take kula da harkokin kasuwanci a kasar Birtaniya ta sanar da cewa; jirgin kasar na kasuwanci ya nutse a cikin ruwan tekun “Red-Sea”.

 Hukumar ta kasar Birtaniya ta ce; A jiya Talata ne dai jirgin ruwan kasar na kasuwanci mai suna;  Totur ya fuskanci kai hari daga nisan mil 66 daga gabar ruwan ‘a-Hudaidah’,ana kuma fuskanatar mamalar mai daga Jirgin ruwan.

Kakakin sojan kasar Yemen Yahya Sarii ya babbatar da kai wa jirgin ruwan na Birtaniya hari, tare da cewa ya kusa nutsewa.

Su dai sojojin kasar Yemen sun shiga cikin masu tare wa Faalsdinawa fada,inda suke hana duk wani jirgin ruwa da ya nufi HKI wucewa ta mashigar ruwan “Babal-Mandab”.

Kasar Yemen ta sha nanata cewa, matukar ana cigaba da kai wa Gaza hare,hare to kuwa za su cigaba da hana jiragen ruwan da suke son zuwa tasoshin jiragen ruwa na HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments