Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakiri Kani ya bukaci kasashen musulmi su yi wani abu a aikace don kawo karshen yaki a Gaza.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a zantawarsa ta wayar tarho da babban sakataren kungiyar kasashen Musulmi ta OIC Hussain Ibrahim Taha a jiya Laraba.
Bakiri ya zanta da babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ta IOC ne kan sabbin al-amuran da suke faruwa a yankin Gaza, sun kuma bukaci kasashen musulmi su yi kokarin ganin sun taka wata rawa a bangaren kawo karshen kissan kiyashin ga al-ummar falasdinu a Gaza.
Bakiri ya yaba da kokarin wasu kasashen duniya don kawo karshen kissan kare dangi a gaza, daga ciki ya ambaci kasar Afirka ta kudu wacce ta shigar da karar a gaban kotun ICC kan HKI, da kuma wasu kasashen Laten Amurka wadanda suka kai ga katse huldar diblomasiyya da HKI.
A na shi bangaren Hussain Taha ya yi allawadai da ta’asan da HKI take aikata a Gaza, ya kuma bukaci kasashen Musulmi su dasuki matakan da suka dace don kawo karshen wannan kissan kare dangi.