Sayyid Sadar Ya Dora Alhakin Ayyukan Dabbancin Yahudawan Sahayoniyya Kan Amurka

Sayyid Muqtada Sadr ya yi dirar mikiya kan Amurka dangane da yadda take goyon bayan keta ‘yanci da tarwatsa al’umma a Falasdinu Jagoran kungiyar Sadar

Sayyid Muqtada Sadr ya yi dirar mikiya kan Amurka dangane da yadda take goyon bayan keta ‘yanci da tarwatsa al’umma a Falasdinu

Jagoran kungiyar Sadar ta Iraki, Sayyid Muqtada al-Sadr, ya jaddada cewa: Batun dimokaradiyya da alkawurran Amurka suna tafiya a ma’auni biyu ne, yadda ya yi nuni da cewa; Amurka da take da’awar kare hakkin bil’adama tana goyon bayan ayyukan ta’addancin ‘yan sahayoniyya a Gaza.

A cikin jawabin da ya gabatar a jiya Laraba, Sayyid Al-Sadr ya bayyana cewa: Duk wata gwamnati ko kasa da zata aikata abin da yahudawan sahayoniyya suka yi, na yin luguden bama-bamai a kan sansanonin ‘yan gudun hijira da barin gawarwakin mata da kananan yara da suka kone a kan hanyoyi saboda wulakanta bil’adama, yadda ke faruwa a Falasdinu gami da yin watsi da dukkan kudurorin Majalisar Dinkin Duniya a idon duniya da al’ummu da kuma kalubalantar hukunce-hukuncen kotun kasa da kasa, da duniya ta ji bambami da gutsiri tsoman Amurka.

Sayyid Sadr ya yi tambayar cewa: Wannan wane irin dimokaradiya da ‘yanci da Amurka take da’awar karewa ta hanyar siyasarta ta munafunci, saboda ta haramta hakan ga wasu amma ta share fage ga ‘yan sahayoniyya suna cin karensu ba babbaka. Yana mai bayyana takaicinsa da cewa: Wannan wace irin dabi’a ce da ta yi hannun riga da adalci da dan Adamtaka? Wace irin nau’in mu’amala ce ta masu girman kai da rashin kunya a wannan zamani!

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments