Shugaban Belarus ya dora alhakin faduwar jirgin shugaba Raisi a kan takunkumin Amurka

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko ya dora alhakin faduwar jirgi mai saukar angulu na shugaba Raisi a kan takunkuman da Amurka ta kakaba wa kasar

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko ya dora alhakin faduwar jirgi mai saukar angulu na shugaba Raisi a kan takunkuman da Amurka ta kakaba wa kasar Iran, saboda rashin shigar da sassan kayayyaki na jiragen helikwafta a cikin Iran.

A yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, Lukashenko ya ce, “A matsayina na mutum, zan ce mummunan matsayi na bakar siyasar Amurka ne ya haifar da haka”.

Ya kara da cewa, “Ina nufin takunkumin, domin kuwa wadannan mutane marasa ‘yan adamtaka ba su da hakkin sanya takunkumi kan jiragen ruwa, jiragen sama, jirage masu saukar ungulu da ke jigilar mutane.

“Sun hana kamfanoninsu yin hidimar helkwaftan Raisi, Don haka abin da ya faru laifinsu ne.”

Shugaban Belarus ya ci gaba da bayyana fatan cewa a karshe Iran za ta “gano abin da ya faru a kan wannan lamari,” kamar yadda ya kira Raisi “mutum na gari wanda ya gudanar da tattaunawa ta gaskiya, ya damu da ci gaban kasarsa da kuma kare muradunta da na mutanensa.”

Shugaban Rasha Putin ya yi tsokaci da cewa, jirage masu saukar ungulu guda biyu da ke tare da shugaba Raisi wani bangare na ayarin shugaban , kuma sun tashi ba tare da wata matsala ta musamman ba a cikin yanayi guda, a kan hanya daya, amma kuma abin da ya faru, ya auku ne kawai a jirgin da yake dake da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments