Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya jinjinawa dakarun sojin ruwa na kasar Iran a ranar dakarun sojin ruwa na kasa, yace jajirtattun dakarun sojin ruwa na kasar su ke kare kasarsu a duk inda ake daga tutar kasar, kana kuma ya girmama wadanda suka yi shahada a jirgin ruwa na Paykan da kuma jirgin yaki na Dena
A cikin sakon da ya aikewa kwamandan dakarun ruwa na kasar iran Rear Admiral shahram irani, iraqchi ya fadi a yau lahadi da safe cewa sadaukarwa da ma’aikatan jiragen ruwa na kasar iran suka yi ta tabbatar da tsaron muradun kasar a bangaren ruwa a duk tsawon tarihinta
Yace daga paykan zuwa Dena akwai gaskiya guda daya da ba zata taba canzawa ba, jaruman ma’aikatan jiragen ruwa na iran su ne masu kare wannan kasa, ba wai kawai a kusa da iyakokinta ba , har ma da duk inda tutar iran take filfilawa
Daga karshe ya bayyana cewa tekun fasha da mashigar Hurmuz a matsayin cibiyar tsaron kasar iran ,ya kara da cewa ayyukan rundunar sojin ruwa sun karfafa matsayin kasar a harkokin yankin dama na kasa da kasa