Yamen Ta yi Tir Da Birtaniya Kan Haramta IRGC

Rahotanni sun bayyana cewa kasar yamen ta tir da matakin da gwamnatin birtaniya take son dauka na sanya dakarun kare juyin musulunci na iran IRGC

Rahotanni sun bayyana cewa kasar yamen ta tir da matakin da gwamnatin birtaniya take son dauka na sanya dakarun kare juyin musulunci na iran IRGC a cikin jerin kungiyoyin da ta kira da yan ta’adda, kuma ta jinjinawa manyan dakarun sojin game da kokarin da suke yi na kare kasar iran

Ministan harkokin wajen kasar yamen ya fitar da bayani kwanaki biyu bayan da fira ministan birtaniya Keir Starmer ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta dauki matakin sanya dakarun kare juyin musulunci na kasar iran a matsayin mai hadari karkashin sabuwar dokar tsaro ta kasa inda za su harmata bada taimakon soji

Dakarun IRGC suna daga cikin masu tasiri wajen yakar makirce-makircen yahudawan sahayuniya  a yankin,  kasashen yamma sun bukaci kasashen larabawa masu rauni da sauran kasashen musulmi  wadanda ke aiki kawai a matsayin kayan aiki don cimma mummunar agendarsu da tsare-tsarensu a yanakin baki daya

Har ila yau ya kara da cewa dakarun kare juyin musulunci suna kare martabar kasarsu da kuma yin nasara kan makirce-makircen da makiya da suke kullawa kan iran dama sauran alummar musulmi.

A cikin yan kwanakin nan dakarun sojin Amurka sun kaddamar da mummunan hari ta sama kan kasar  iran sannan suka toshe tashoshin jiragen ruwan iran, wanda hakan ya sabawa yarjejeniyar tsaigaita wuta da aka kulla, sai dai dakarun sojin kasar iran sun mayar da martani mai tsananin kan muradun Amurka dake fadin yankin baki daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted