Imam Sayyid aliyul Khaminaee jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran kuma babban kwamnadan sojojin kasar ya gana da wasu daga cikin manya manyan kwamandojojin sojjin kasar a karon farko tun farmakin ‘waadussaduk’ wanda suka kai kan HKI a ranar 14 ga watan Afrilu da muke ciki.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Imam Khaminaee yana fadawa kwamandojin kan cewa, All..basa sabawa alkawarinsa, na taimakawa muminai, don haka nasara ta muminai ne a duk inda suke.
Jagoran ya kara da cewa hare haren da suka kai kan HKI ya fidda JMI da kuma cikekken matsayinta a idanun kasashen duniya. Ya kuma kara da cewa hare haren sun tabbatar da matsayin mutanen kasar Iran da dagewarsu wajen kare addinin musulunci da kuma taimakawa wadanda aka zalunta.
A wani bangare na jawabinsa jagoran ya taya sojojin da kuma dakarun IRGC zagayowar ranar kafa su. Ya kuma kamala da cewa, aiki bai kare ba, dole sojojin kasar su nemi hanyoyin kara martaba da matayin makaman kasar .
Kafin haka Janar Muammad Bakiri kwamnadan sojojin kasar ya bayyana irin ci gaban da sojojin kasar suka samu a shekara ta 1402 da ta gabata, daga ciki har da ‘yakin Tufanul Aksa’ da kuma hare haren ‘Waadussadik’.