An sanya gawar jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaei, a makwancinsa na kasarshe kusa da hubbaren Imam Aliyu bin Musa Arrudha da ke arewa maso gabacin kasar Iran bayan kwanaki na tarurrukan bankwana da salloli a Tehran, Qom da kuma kasar Iraki a safiyar Yau Jumma’a.
Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya ce miliyoyin mutane masoya daga ciki daga wajen kasar sun halarci taron bankwana da limamin a birnin Mashad a jiya Alhamis, inda aka yi masa sallah ta karshe sannan aka sanya shi a makwancinsa na karshe.
Manya manyan jami’an gwamnatin kasar Iran wadanda suka hada da kakakin majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibaf, alkalin alkalai Gholam Hussain Mohsen Ejei, tsohon mataimakin shugaban kasa Mohammad Mokhbir, da limamin masallacin jumma’a na birnin Mashsd Aya. Seyed Ahmad Alamolhoda da sauransu.
A Mashad dansa Aya. Mustafa Khaminaei ne ya jagoranci sallah kan mahaifinsa. Kuam an sanyashi a wani wuri da ake kira Darudhikir cikin Haramin.
Gwamnatin kasar Iraki ta bada sanarwan cewa mutanen kasar kimani miliyon 10 ne suka halarci Jana’izar Jagodan a kasar, akuma birnanen Najaf da Karbala.