Ofishin Jakadancin Iran A Turkiyya Ta Yi Watsi Da Jawabin Bayan Taron Kungiyar NATO

A wani bayanin maida martani ga bayanin bayan taro na kungiyar tsaro ta NATO a birnin Ankara babban birnin kasar Turkiya, ofishin jakadancin Jumhuriyar musulunci

A wani bayanin maida martani ga bayanin bayan taro na kungiyar tsaro ta NATO a birnin Ankara babban birnin kasar Turkiya, ofishin jakadancin Jumhuriyar musulunci ta Iran ta yi watsi da jawabin bayan taro na kungiyar dangane da shirin nukliyar kasar Iran da kuma kwace mashigar ruwa ta Hurmuz da ta yi.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto bayanin yana cewa kungiyar NATO ta yi haka ne don siyasa da kuma goyon bayan Amurka da HKI a yakin da suka dorawa JMI suke kuma ci gaba da keta yarjeniyar dakatar da yaki da aka cimma da su.

Martanin ya kara jaddada cewa shirin Nukliya na kasar Iran na zaman lafiya ne kuma babu bangaren soje a cikinsa. Banda haka martani ya kara da cewa, kasar Iran mamba ce a yarjeniyar NPT kuma ita ce kasa tilo a duniya wacce hukumar IAEA ta fi yi mata bincike.

A wani bangare ofishin jakadancin ya kara da cewa, kasar Iran tana da kekyawan tarihi a samar da zaman lafiya a zirga-zirgan jiragen  ruwa a tekun farisa da kuma mashigar ruwa ta Hurmuz, amma yakin tsokana wanda Amurka da HKI suka dorawa kasar ne ya rikita zaman lafiya a wadannan wurare.

Ya kuma kammala da cewa Amurka da HKI ne suka bude wuta kan teburin tattaunawa na a baya da kuma yanzu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted