Isra’ila Ta Hana Sakataren Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Kai Ziyara Yankin Falasdinu

kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta bayyana cewa gamnatin yahudawan sahyuniya ta hana sakatare janar dinta Nabil Fahami kai ziyara yammacin kogin jodan da aka

kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta bayyana cewa gamnatin yahudawan sahyuniya ta hana sakatare janar dinta Nabil Fahami kai ziyara yammacin kogin jodan da aka mamaye, wanda aka shirya zai kai a jiya laraba a matsayin ziyararsa ta farko tun bayan samun wannan mukami a farkon watan da muke ciki

mai Magana da yawun sakatare janar din kungiyar ya fadi cewa lallai gwamnatin falasdinu ta sanar da kin amincewar isra’ila na ziyarar da aka sanya fahimi zai kai yankin falasdinu domin kara karfafa alummar falasdinu da kuma ganawa da shugaban gwamnatin kwarya kwaryan cin gashin kai ta falasdinu Mahmud Abbas Abu Mazin

Haka zalika ya bayyana a cikin jawabin nasa cewa sakataren kungiyar ya zabi yankin falasdinu ya zama inda zai fara kai ziyararsa a kasashen ketare ne ganin yadda lamarin falasdinu ya zama shi ne a kan gaba, kuma ya jaddada cewa za ta ci gaba da zama ta gaba-gaba a kasashen larabawa.

daga karshe yayi nuni game da wajibcin daukar mataki kan Isra’ila game da tauye hakkin falasdinawa da take yi ,yace lallai kare hakkin kafa kasashe biyu masu cin gashin kai yana bukatar zage damtse daga dukkan kasashen dake goyon bayan zaman lafiya na adalci don takawa isra’ila burki. da kuma taimakawa falasdinawa da suke fuskantar matsaloli fiye da kowanne lokaci a baya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted