Rundunar kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) ta ce ta kai jerin hare hare kan wuraren soji 85 na Amurka a kasashen Bahrain da Kuwait da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki a matsayin martani na farko ga harin da Amurka ta kai wa kasar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar Rundunar IRGC, ta ce hare-haren an kai su kan tashar Salman, da ta kunshi rundunar sojin sama ta biyar ta Amurka a Bahrain, da kuma sansanin sojin sama na Ali Al Salem da ke Kuwait.
Ta kuma sanar da kakkabo wani jirgin sama mara matuki samfarin MQ-9.
Mai magana da yawun IRGC, Birgediya Janar Hossein Mohammadi, ya ce an harbo jirgin mara matuki a lardin Bushehr da ke kudancin kasar bayan hare-haren jiragen saman Amurka da daddare.
Sanarwar ta zo ne bayan da Amurka ta kaddamar da wani sabon hari na soji a kan “sansanonin bakin teku da tashoshin da ba na soja ba” a lardin Hormozgan da ke kudancin Iran da Mahshahr, wanda IRGC ta ce “ya karya yarjejeniyar tsagaita wuta a fili” kuma ya keta yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad”.