Fira Ministan Kasar Denmark Ta Fada Wa Donald Trump Cewa Yankin Greenland Ba Na Sayarwa Ba Ne

Fira ministar kasar ta Denmark  Mette Frederiksen ta fada wa shugaban kasar Amurka Donald Trump cewa yankin Greenland ba na sayarwa ba ne. Fira ministan

The Prime Minister Mette Frederiksen is meeting with the leaders of the European Union //

Fira ministar kasar ta Denmark  Mette Frederiksen ta fada wa shugaban kasar Amurka Donald Trump cewa yankin Greenland ba na sayarwa ba ne.

Fira ministan ta kasar Denmark  Mette Frederiksen  wacce take halartar taron kungiyar yarjejeniyar tsaro ta “Nato” tana mayar da martani ne ga sabon furucin da ya fito daga bakin Donald Trump akan tsibirin dake cin kwarya-kwaryar gashin kai a karkashin kasar Denmark.

Haka kuma ta fadi cewa; Na saurari abinda shugaban kasar Amurka ya fada a jiya Talata, don haka matsayar Amurka a fili take akan wannan batun, da hakan abin takaici ne.”

Shi dai Donald Trump ya fada a jiya Talata cewa; Ya kamata a ce yankin na Greenland yana a karkashin kasar Amurka ne, ba a karkashin kasar Denmark ba.” Sai dai a wannan karon shugaban kasar ta Amurka bai yi barazana da amfani da karfi ko kudi ba domin shimfida ikon kasarsa akan Greenland, kamar yadda ya yi a baya.

 Donald Trump wanda yake halartar taron kungiyar ta “Nato” a kasar  Turkiya, ya bayyana cewa; Batun nay akin Greenland ya haddasa sabani a tsakanin kasarsa da kungiyar ta Nato. Trump ya ce yankin na Greenland yana da muhimmanci ga kasar Amurka, kuma jiragen ruwan Rasha da China suna zagaye da shi, amma kuma Nato ba za su amince da mu ba duk da yawan kudaden da muke kashewa wajen fada da Rasha. Yankin na Greenland yana cike da ma’adanai da albarkatun masu wuyar samu, da hakan ya sa Amurka take da kwadayin shimfida ikonta a cikinsa

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted