An bude kofofin babban zauren hubbaren Imam Khomeini (Allah Ya yarda da shi)… kuma masu makoki suna ci gaba da kwarara zuwa hubbaren
Jama’a sun fara taruwa a wurin da ake yin juyayin bankwana da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Shahidi Ayatullahi Sayyid Ali Khamene’i, bayan bude kofofin babban zauren hubbarten Imam Khomeini (RA) da ke birnin Tehran.
An bude kofofin babban zauren hubbaren Imam Khomeini (RA) a lokaci guda tare da kiran sallar asuba ga wadanda ke son yin ziyarar karshe da kuma yin bankwana da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci shahidi Ayatullahi Sayyid Ali Khamene’i {Allah Ya yarda da shi}.
Masu halartar da ke jiran fara bikin bankwana da Jagoran Juyin juya Halin na Musulunci shahidi na kasa Ayatullahi Sayyid Khamene’i sun yi sallar asuba cikin jam’i a Hubbaen kuma sun ci gaba da zama a wurin suna jiran shirin da aka shirya gudanarwa, wanda aka tsara zai fara cikin kasa da awanni uku.
Za a fara bikin bankwana da Jagora juyin juya halin Musulunci shahidi Ayatullah Imam Sayyid Ali Khamenei, a safiyar yau, Asabar, 4 ga watan Yulin shekara ta 2026, da karfe 6:00 na safe kuma za a ci gaba da shi har zuwa karfe 8:00 na dare a ranar Lahadi, 5 ga watan Yuli.
An shirya yin sallar jana’izar Jagora shahidi a safiyar ranar Lahadi.Daga nan za a dauki gawar zuwa birnin Qum a ranar Talata, domin gudanar da jana’iza da addu’o’i.
Bayan nan a ranar Laraba, 8 ga Yuli, za a kai gawar zuwa birnin Najaf don yin dawafi da kuma yin jana’iza a hubbaren Imam Ali dan Abi Talib (A.S). Za a yi irin wannan bukukuwa juyayi a hubbaren Imam Hussein (A.S) da ɗan’uwansa Abu al-Fadl al-Abbas (A.S) da ke Karbala.