Shugabanni da jami’ai daga ƙasashe 40 ne zasu halarci jana’izar Marigayi Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran da ya yi shahada
Iman Attarzadeh, mai magana da yawun jana’izar marigayi Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei (Allah Ya yi masa rahama), ya sanar da cewa: shugabanni da jami’ai daga kusan ƙasashe 40 ne za su halarci juyayin alhini don girmama Jagoran da aka yi wa masa kisan gilla.
Attarzadeh ya yi nuni da cewa: Manyan mutane da shugabannin ƙasashen ƙasashen waje zasu halarci jana’izar, yana mai cewa: “Baya ga halartar jama’a da yawa, manyan mutane na siyasa, al’adu, kimiyya, addini, da na ilimi, da kuma manyan mutane daga ko’ina cikin duniya, za su halarci jana’izar da kuma gudanar da juyayi da alhini na bankwana don girmama jagoran juyin juya halin na Musulunci da aka yi wa kisan gilla a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran.”
Ya ƙara da cewa: “Shugabanni da manyan jami’ai daga kusan ƙasashe 40 za su halarci waɗannan taron juyayi don girmama Jagoran da aka yi wa kisan gilla.”
Mai magana da yawun jana’izar ya yi nuni da cewa nan ba da jimawa ba jami’an Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran za su sanar da cikakkun bayanai game da matakin wakilai, ƙasashen da suka halarta, da sunayen waɗanda suka halarci taron.