Bayan karar da wasu mutane 15 su ka shigar a wata kotu a nan Iran, saboda yadda aka tsare su gabanin juyin juya halin musulunci, an zargi Amurka da hannu wajen kafa kungiyar leken asiri ta “ Savak”, wacce ta rika azabtar da fursunoni a zamanin tsarin sarauta na Iran.
Kotun ta yanke hukunci akan cewa Amurka ta biya mutanen da su ka shigar da karar kudin da su ka kai dalar Amurka miliyan 91 a matsayin rage zafin cutar da su da aka yi.
A yayin zaman kotun an gabatar da takardu na shaida akan cewa Amurka tana da cikakkiyar masaniya akan halayyar keta ta gwamnatin Sha da kuma rashin ‘yan’adamtaka.
Dukkanin wadanda su ka shigar da karar ‘yan gwgawarmaya ne a Iran wadanda su ka yi fada da gwamnatin kama-karya ta Pahlavi.