Bayanai da dakarun kare juyin juya halin Musulinci na iran suka fitar ya nuna cewa kasar ta samu nasarar cike gibin makamai masu linzami da na jiragai marasa matuka a lokacin yarjejeniyar tsagaita wutar makonni biyu da aka cimma.
Janar Seyyed Majid Mousavi, kwamandan rundunar sojin sama ta juyin juya halin Musulunci (IRGC), ya yi ikirarin cewa kasar ba wai kawai ta samu nasarar cike gibin makamai masu linzami da na jiragai marasa matuka ba a lokacin yarjejeniyar tsagaita wutar, har ma ta wuce karfinta kafin yakin.
Janar din ya raba wani bidiyo a dandalin UpScrolled a ranar Lahadi, yana nuna makamai masu linzami da na jiragai marasa matuka.
Sakon da ke tare da bidiyon ya jaddada cewa samar da makamai masu linzami da na jiragai marasa matuka ya wuce karfinta kafin yakin.”
Wadannan kalamai sun zo ne yayin da rahotanni da dama suka saba wa ikirarin cewa hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran na tsawon makonni sun raunana karfin shirin makamai masu linzami na kasar sosai.
Jaridar Wall Street Journal, ta ambato hukumomin leken asiri na Amurka, na cewa Iran har yanzu tana da “dubban makamai masu linzami masu cin matsakaici da gajere zango a karkashin kasa.”