Sakon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ga Malaman Ahlus-Sunna Na Lardin Hormozgan

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya nuna godiya da kuma jinjinawarsa ga malaman Ahlus- Sunna saboda girmamawa da biyayyarsu ga jagorancin kasa A cikin wani

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya nuna godiya da kuma jinjinawarsa ga malaman Ahlus- Sunna saboda girmamawa da biyayyarsu ga jagorancin kasa

A cikin wani sako da ya aike wa malaman Ahlus-Sunna a lardin Hormozgan da ke kudancin Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Seyyed Mojtaba Khamenei, ya nuna godiyarsa ga malaman addini da dalibai mabiya tafarkin Ahlus-Sunna na lardin Hormozgan saboda tausayawar da suka nunawa ‘yan uwansu musulmi da biyayyarsu ga jagorancin kasa.

A cikin sakonsa, Jagoran ya nuna godiyarsa ga tausayi da kyautatawa da suka nuna wajen yin ta’aziyya kan shahadar marigayi Jagoran Addini, Ayatullah Seyyed Ali Khamenei. Wakilin Jagoran Addini a lardin Hormozgan, Hujjatul-Islam Mohammad Abadi Zadeh, ya sanar da karbar sakon, yana mai jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin al’ummar Musulmi.

Hujjatul-Islam Abadi Zadeh ya bayyana cewa: Sakon daga Jagoran juyin juya halin Musulunci yana da matukar muhimmanci kuma an fitar da shi ne a cikin tsarin karfafa jituwa tsakanin al’ummar kasa, karfafa tausayi, da kuma zurfafa dangantaka tsakanin sassa daban-daban na al’ummar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted