Jami’in Iran: Iran Ta Yi Watsi Da Duk Wani  Alkawarin Da Ya Sabawa Dokokin Duniya

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran ya  jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da duk wani alkawari da ya saba wa dokokin duniya

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran ya  jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da duk wani alkawari da ya saba wa dokokin duniya

Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Iran Sa’id Khatib-zadeh ya jaddada cewa: Shugaban Majalisar Shawarwari ta Musulunci (wato Majalisar Dokoki) da Ministan Harkokin Waje sun bayyana a taronsu na baya-bayan nan cewa: Shawarwarin da aka gabatar wa ɗayan ɓangaren suna da adalci kuma masu amfani, suna nuna haƙƙin a’ummar Iran.

A wata hira da suka yi da Hukumar Rediyo da Talabijin ta Iran (IRIB), Khatib-zadeh ya bayyana cewa: Tawagar Iran a zaman tattaunawan diflomasiyya tana ɗaukar matakai masu inganci a lokacin yaƙi da Amurka da ‘yan Sahayoniyya suka ƙaƙabawa Iran, baya ga tattaunawar da ake ci gaba da yi game da shiga tsakani da Pakistan  ke yi.

Khatib-zadeh ya jaddada muhimmancin tsayin daka da goyon bayan al’ummar Iran ga ƙasar game da zaluncin ‘yan Sahayoniyya da Amurka, yana mai lura da cewa: Mutane ba su da wani zaɓi illa su taimakawa wannan gwagwarmayar ƙasa. Ya kuma soki kalaman shugaban Amurka masu karo da juna, yana mai tabbatar da cewa; Dabarun Jamhuriyar Musulunci ba su dogara akan irin waɗannan kalamai ba.

Ya jaddada cewa: Diflomasiyya ita ce kawai mafita ga kowane rikici, kuma ya sake nanata ƙin amincewa da duk wani alƙawarin da ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted