A cewar kafafen yada labarai na yankin , rikici ya barke tsakanin dakarun Pakistan da Afganistan a yankin kan iyakarsu, inda aka kai hare-hare ta sama daga bangarorin biyu . Ministan Tsaron Pakistan ya bayyana cewa kasarsa ta shiga “yakin fili” da Afganistan .
Dangane da wannan tabarbarewar, Jamhuriyyar Musulunci ta Iran ta nuna damuwa matuka game da tashe-tashen hankula da ke faruwa tsakanin kasashen biyu makwabta . A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya jaddada cewa a wannan watan Ramadana mai albarka, lokaci ne na kamewa da kuma karfafa hadin kan al’ummar Musulunci . Don haka yana da muhimmanci kasashen biyu su magance sabani a tsakaninsu ta hanyar tattaunawa cikin kyakkyawar makwabtaka .
Iran ta kuma bayyana cikakkiyar shirinta na yin sulhu da kuma ba da duk wani taimako da ake bukata domin gudanar da tattaunawa tsakanin Pakistan da Afganistan, da kuma inganta fahimtar juna da hadin gwiwa a tsakaninsu . Wannan ba shi ne karon farko da Iran ta bayar da damar yin sulkuwa ba tsakanin kasashen biyu .
A cewar sanarwar Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, wannan rikici ba wai kawai zai janyo asarar rayuka da dukiya ba, har ma zai kara ta’azzara rashin tsaro a yankin baki daya . Iran ta bukaci bangarorin biyu da su mutunta yankin juna da kuma ‘yancin cin gashin kansu, kuma ta jaddada goyon bayanta ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin .