Ministan Harkokin Wajen Oman, Badr al-Busaidi, ya sanar da kammala zagayen tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a birnin Geneva a wannan Alhamis, tare da samun babban ci gaba.
Ministan Harkokin Wajen Oman ya bayyana cewa, za a gudanar da tattaunawa a matakin kwararru a mako mai zuwa a birnin Vienna. Ya kuma tabbatar da cewa za a ci gaba da tattaunawar nan ba da jimawa ba bayan tuntubar kasashen da abin ya shafa.
Al-Busaidi ya bayyana godiyarsa ga dukkanin wadanda suka yi ƙoƙari a wannan batu, da kuma hukumar makamashin nukiliya ta duniya da kuma gwamnatin Switzerland mai masaukin baki.
A nasa bangaren, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqaei, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Iran (IRNA) cewa an kammala mataki na biyu na zagaye na uku na tattaunawar nukiliya a Geneva.