Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baghaei ya zargi kasashen Amurka da HKI da amfani da salon sojojin Nazi na kasar Jamus a wajen yada karya da farfaganta dangane da shirin Nukliyar kasar Iran da kuma karfin makamanta masu linzami. Da kuma kan yawan mutanen da aka kashe a rikicin farkon wannan shekarar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Baghaei yana fadar haka a jiya Laraba, ya kuma bayyana cewa wannan yana faruwa ne a dai dai lokacinda tattaunawa dangane da shirin makamashin nukliya na kasar Iran yake ci gaba tsakaninta da Amurka a Geneva. Da kuma yiyuwar Amurka ta farwa kasar da yaki.
Yace: Ka’idar ‘a rika maimaita karya ya isa ya maida karyar gaskiya’ ta Jpseph Goebbels ne na jam’iyyar Nazi ta kasar Jamus, ya ce a halin yanzu gwamnatin kasar Amurka tana amfani da wannan ka’idar haka ma HKI, don cimma manufofinsu a kan kasar Iran. Har’ila yau da kuma boye kissan kiyashin da HKI ta aikata kuma tace ci gaba da aikatawa a gaza da kuma kasar Falasdinu da aka mamaye.
Baghaei ya bayyana cewa dukkan labaran da suke yadawa dangane da shirin nukliyar kasar Iran da makamanta masu linzami har’ila yau da abinda ya faru a rikincin farkon wannan shekarar duk yana karkashin shirin ‘manyan karyaki’ da suke yadawa ne. Yace wannan tarin manya-manyan karkayki ne guda uku wadanda suka sanya a gaba. Inji shi.
Shirin nukliyar Iran ya wuce mizanin zaman lafiya, makamai masu linzamin Iran masu keta nahiyoyi ne ko kum,a yawan mutanen da aka kashe a Iran a rikicin baya bayan nan suna dayawa. Trump da bakinsa yana fadar cewa yawan mutanen da aka kashe a rikicin watan Jeneru 32,000 al-hali a wajen gwamnatin Iran bai fi 3,117 ne.