Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya bayyana cewa tattaunawa tsakanin Iran da Amurka na ci gaba babu kakkautawa a birnin Geneva, inda aka tsaida tattaunawa na wani lokacin don tuntubar cibiyoyin kasashen kan wasu al-amura na karamin lokaci.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Baghaei yana fadar cewa a zaman farko bangarorin biyu sun tattauna sun kuma yi musayan ra’ayi kan shirin nukliyar kasar Iran da kuma batun dauke mata takunkuman tattalin arziki. Sannan a halin yanzun ma bayan hutu a wani lokaci ana ci gaba da tattaunawa.
Sannan tattaunawar kamar yadda muka bayyana kan shirin makamashin nukliyar kasar Iran ne kawai da kuma batun dauke mata takunkuman tattalin arziki. Babu batun makamai masu linzami na kasar ko kuma siyasar Iran a gabas ta tsakiya.