Geneva : An bude zagaye na 3 na tattaunawar nukiliya tsakanin Iran da Amurka

An fara tattaunawa tsakanin Amurka da Iran kan shirin nukiliyar Tehran, a zagaye na uku a ofishin jakadancin Oman da ke birnin Geneva na kasar

An fara tattaunawa tsakanin Amurka da Iran kan shirin nukiliyar Tehran, a zagaye na uku a ofishin jakadancin Oman da ke birnin Geneva na kasar Switzerland.

Rahotanni sun ce Ministan Harkokin Wajen Oman Sayyid Badr bin Hamad Al Busaidi ya gabatar da shawarar Iran ga Amurka, kodayake ba a bayyana cikakken bayani game da abubuwan da ke ciki a hukumance ba.

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi, wanda ya isa Geneva ranar Laraba, shi ne ya jagoranci tawagar Iran.

Bangaren Amurka yana karkashin jagorancin manzon musamman na Amurka Steve Witkoff da surukin Shugaba Donald Trump, Jared Kushner.

Kafin tattaunawar, Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Mariano Grossi da ministan harkokin wajen Oman sun gana don tattauna batutuwan fasaha da suka shafi shirin nukiliyar Iran.

Da yake magana da manema labarai a Geneva, mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Esmail Baghaei ya ce masu shiga tsakani na Iran sun shiga tattaunawar da cikakken shiri.

Ya ce tawagar Iran ta kunshi kwararru a batutuwan nukiliya da harkokin tattalin arziki.

Ya kara da cewa, “Mun shirya tsaf kuma mun kuduri aniyar ci gaba da tattaunawar har tsawon lokacin da ya dace,” in ji shi.

Iran dai na kallon wannan tattaunawa a matsayin wani gwaji ga Amurka idan da gaske ta ke kan cimma matsaya da ita.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted