Jakadan din din din na kasar Iran a majalisar dinkin duniya ya nuna adawarsa a fili game da daftarin kudurin majalisar kan rikicin kasar Ukrain, saboda ba zai taimaka wajen samar da tabbataccen zaman lafiya mai dorewa ba.
Ali Bahraini jakadan iran na din din din na kasar Iran a majalisar dinkin duniya a birnin janeva ya jadda matsayar iran game da rikicin kasar Ukrain a zama na 23 da babban zauren majalisar dinkin duniya yayi a jiya talata ya jaddada bukatar da ake da ita na tattaunawar zaman lafiya da kuma aiki da dokokin kasa da kasa.
yana cewa tun bayan fara rikicin, iran ta bukaci dukkan mambobin majalisar da su mutunta yanci da hadin kai na kasar kuma su guji yin amfani da barazana ko karfi akan lamarin. haka zalika tawagar Iran ta nuna damuwa sosai game da manufofin dake bayan kudurin, tana mai nuna cewa yana iya zama yafi karfi wajen cimma manufofin siyasa a yankin mai makon karfafa sulhu a kasar Ukraian