Kungiyar Jihadun -Islami ta bayyana cewa: “Majalisar Zaman Lafiya” a Gaza wasan kwaikwayo ne kawai da aka shirya
Mataimakin Sakatare Janar na Ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Jihadul-Islami, Muhammad al-Hindi, ya bayyana cewa: “Majalisar Zaman Lafiya” a Gaza wasan kwaikwayo ne da bai hana gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila ci gaba da yaƙin kawar da Falasdinawa a yankin ba.
A cikin sanarwar manema labarai a ranar Talata, al-Hindi ya ƙara da cewa: “Majalisar Zaman Lafiya,” wadda shugaban Amurka Trump ke jagoranta, ta amince da ajandar ‘yan mamaya kuma tana neman tabbatar da tsaron yankunan da aka mamaye ne kawai.
Ya lura cewa kalaman Jakadan Amurka Huckabee sun nuna son kai da Amurka ke nunawa ga yankin da ke mamaye. Ya jaddada cewa da ya fi dacewa gwamnatin Amurka ta yi Allah wadai da kuma neman afuwa ga kalaman Jakadanta Huckabee.