Duniya na ci gaba da tir da Isra’ila kan shirin mamaye Yammacin Kogin Jordan

Kasashen duniya na ci gaba da yin tir da Allah wadai da Isra’ila kan shirinta na mamaye gabadayen yammacin kogin Jordan. A baya bayan nan

Kasashen duniya na ci gaba da yin tir da Allah wadai da Isra’ila kan shirinta na mamaye gabadayen yammacin kogin Jordan.

A baya bayan nan kusan kasashe 20 ne sukayi Allah wadai da Isra’ilar saboda fadada ikonta a Yammacin na Kogin Jordan, inda sukayi gargadin cewa wadannan ayyukan suna da nufin wargaza yiwuwar kafa kasar Falasdinu da kuma canza fasalin yankin na har abada.

A baya bayan nan ne dai, Isra’ila ta dauki matakai da dama, wadanda ministocin ‘yan ra’ayin mazan jiya suka goyi baya, don karfafa ikonta a kan Yammacin Kogin Jordan, gami da kaddamar da wani tsari na yin rijistar filaye a Yammacin Kogin Jordan a matsayin “kadarar gwamnati” da kuma ba wa Isra’ilawa damar siyan filaye kai tsaye a can.

“Irin wadannan ayyuka sun kunshi karan kai tsaye ga wanzuwar kasar Falasdinu da kuma aiwatar da mafita ta samar da kasashe biyu inji kasashen.

Sun kuma yi kira ga gwamnatin Isra’ila “ta soke wadannan shawarwarin nan take” ta kuma mutunta dokokin kasashen duniya.”

Daga cikin wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar akwai Saudiyya, Brazil, Masar, Spain, Indonesia, Turkiyya, da Faransa.

Shirin ya kuma sami goyon bayan sakatarorin kungiyar kasashen Larabawa da kungiyar Hadin Kan kasashen Musulmi, da kuma Hukumar Falassinu.

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da sanarwar kasashen , inda ta kira ta a mastain “mataki mai kyau na adawa da shirye-shiryen fadada tsarin mulkin mallaka, wanda hakan ya zama keta dokokin kasa da kasa da kuma kudurorin MDD.Rahotanni : Babban Janar din Trump ya yi gargadi game da hadarin

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted