Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baghaei yayi watsi da jita -jitar da ake yadawa game da yarjejeniyar wucin gadi kan shirin ta na nukiliya yace wannan batun bashi da tushe balle madafa, adaidai lokacin da Tehran ta shirya domin fara tattaunawa ta gaba A janeva.
wannan tsokaci ya zo ne kwanaki 2 kafin wakilan iran da kasar Amurka su fara tattaunawa a kasar Switland, jami’an iran sun fadi cewa tattaunawar yanzu ta mayar da hankali ne a musayar bayanai a rubuce, tehran ta jaddada cewa cire mata takunkumin zalunci shi ne babban muradunta.
ana sa bangaren ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya sanar cewa tattaunawarsu ta gaba da kasar Amurka za ta kasance a ranar Alhamis mai zuwa a birnin janeva na kasar Switzland , agendar zaman da aka yi a baya a muskat da na janeva ta mayar da hankali ne kan batun shirin nukiliya da kuma cire mata takunkumin zalunci da Amurka ta kakaba mata