Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna sa ido sosai kan duk wani motsin Amurka
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: “Har yanzu suna sa ido sosai kan ayyukan Amurka, kuma sun yi duk shirye-shiryen da suka wajaba don fuskantar duk wani yanayi mai yiwuwa.”
Pezeshkian ya rubuta a cikin wani rubutu a dandalin X nasa da Turanci: “Iran ta himmatu ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Tattaunawar da aka yi kwanan nan ta haɗa da musayar shawarwari masu amfani da kuma alamun ƙarfafa gwiwa.”
Shugaban Iran ya ƙara da cewa: “Duk da haka, har yanzu suna sa ido sosai kan ayyukan Amurka, kuma sun yi duk wasu shirye-shiryen da suka dace don duk wani yanayi mai yiwuwa.”