Matawalle ya yi wannan alkawari ne a lokacin da ya ziyarci masana’antar Briech UAS da ke Kuje, a gefen Babban Birnin Tarayya.
A cikin wata sanarwa da Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Yada Labarai, Ahmad Dan Wudil, ya fitar, ministan ya ce gwamnati ta samar da tsare tsare da za su bai wa kamfanonin cikin gida fifiko wajen saye da kwangiloli.
Ya ce, “Gwamnatin Najeriya ta fahimci bukatar bai wa kamfanonin cikin gida damar bunkasa.”
Ya kara da cewa yanzu ya zama wajibi ga ma’aikatun gwamnati da hukumomi su fara duba yiwuwar samun kaya da ayyuka daga kamfanonin Najeriya kafin su nemi na kasashen waje.
“Dole ne kafin a duba waje, a fara tantance ko akwai kamfanin Najeriya da zai iya samar da kayayyaki ko ayyukan da ake bukata,” in ji Matawalle.
Ministan ya kuma bukaci kamfanin da ya fadada harkokinsa zuwa kera makamai da harsasai, bisa ajandar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na rage dogaro da kayan aikin soja daga kasashen waje.
“Gwamnatin Tarayya a shirye take ta rika tallafawa da sayen kayayyakin masana’antun cikin gida,” in ji shi.
Matawalle ya bayyana cibiyar a matsayin abin burgewa, yana mai cewa tana kera jiragen sama marasa matuki na cikin gida, ciki har da na leken asiri, sa ido da tattara bayanai, da kuma jiragen yaki.
A yayin zagayen, Shugaban kamfanin, Bright Echefu, ya nuna wasu samfurori da aka kera a gida, ciki har da Damisa Combat Drone da aka kirkira domin tattara bayanan sirri da yaki da ta’addanci.
Sauran kayayyakin da aka nuna sun hada da Arsenio BFLY da Xander jiragen leken asiri, da kuma jiragen yaki masu iya aiki a wurare masu wahalar shiga.
Echefu ya ce jiragen kamfanin duk an kera su ne dari bisa dari a Najeriya, kuma ma’aikatan kamfanin duk ‘yan Najeriya ne.
“Babu wani bako a kamfaninmu; dukkan ma’aikatanmu ‘yan Najeriya ne,” in ji shi.
Ya danganta ci gaban kamfanin da goyon baya da sayen kayayyaki da rundunar sojin Najeriya ke yi.
Ministan ya nuna gamsuwa da yadda ake tafiyar da cibiyar, inda ya yaba wa shugabanni da ma’aikata, tare da yin alkawarin ci gaba da tallafa wa masana’antun tsaro na cikin gida.