Mataimakin sipeton rundunar Khatamul Anbiya Burgediya Janar Mohammad Jadar Asadi, ya bayyana cewa samuwar sojojin Amurka a yankin Asia ta yamma ba wasa bane, kuma samuwar jiragen yaki na Amurka a yankin saboda farwa kasar Iran da yaki ne, banda haka, kawa ya san cewa jiragen yakin Amurka sun zo yankin na makonnin da suka gabata don farwa kasar Iran da yaki.
Janar Asadi ya ce jagoran juyin juya halin musulunci ya bayyana gaskiyar magana a inda yake fada “Lalle jirgin yaki mai daukan jiragen yaki yana da hatsarin gaske, amma abinda ya fishi hatsari shi ne makamin da zai kaishi karkashin ruwa’.
Janar Asadi ya bayyana cewa, makiya sun kasa kifar da JMI shekaru fiye da 47 dasuka gabata, kuma muna fatan a halin yanzu ba Amurka da Ingila da Faransa da Jamus da kuma HKI zasu gushe daga yankin yammacin Asia.
Sannan ya kara bayyana cewa, sojojin kasar Iran a shirye suke su kare kasar daga dukkan makiya wadanda suka kuskura suka farwa kasar da yaki.