Rundunar Sojojin Ruwa ta dakarun kare juyin juya halin Musulinci na Iran, ta yi nasarar harba wani makamin garkuwa daga hare haren sama na Sayyad-3G a wani lokacin atisaye a Mashigin Hormuz.
An harba makamin daga jirgin Shahid Sayyad Shirazi, wanda hakan ya zama karo na farko da aka gwada harba irin wannan tsarin a teku.
Sayyad-3G, nau’in makamin kare jiragen ruwa na Sayyad-3 na Iran, yana da tsarin harbin jiragen sama a nisan kilomita 150.
A cewar jami’an Iran, wannan makamin yana ba da kariya daga jiragen sama na matsakaici da dogon zango da kuma zama garkuwa ga tsaron sararin samaniya.
Hukumomin Iran sun tabbatar da cewa wannan makami mai linzami yana karfafa karfin tsaron teku na sojojin ruwan Iran.
Wannan sabon gwajin yana nuna kokarin da Iran ke ci gaba da yi na karfafa tsarin tsaron sama musamman a yankunan teku.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta nuna damuwa game da yiyuwar barkewar tashin hankali a yankin saboda barazanar da Amurka ke yi na kai wa Iran saboda shirinta na nukiliya da sauransu.
Amurka ta tura jiragen ruwan yaki a tekun yankin kusa da Iran, wanda hakan ya sa jami’an Iran suka yi gargadin cewa duk wani hari da za a kai wa kasar zai haifar da babban martani ga muradun Amurka a yankin.