Majalisar Dinkin Duniya ta jadadda cewa: Ci gaba da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ya zama dole domin kauce wa rashin zaman lafiya
Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stéphane Dujarric ya sanar da cewa: Kungiyoyin kasa da kasa sun tabbatar da goyon bayansu ga ci gaba da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka.
Da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis game da karuwar sojojin da ke yankin Tekun Fasha, kakakin ya ce, “Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, kamar sauran mutane, yana matukar damuwa game da karuwar kasancewar sojoji da kuma yadda suke gani.”
Kakakin ya jaddada cewa, “Wannan shi ne dalilin da ya sa suka karfafa tare da yin kira ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka da su ci gaba da tattaunawarsu, wacce Sarkin kasar Oman ke shiga Tsakani tare da taimaka musu.”
An gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar makamashin nukiliya tsakanin Iran da Amurka a Geneva, Switzerland, ranar Talata, inda aka kammala bayan kimanin sa’o’i uku da rabi na tattaunawa mai zurfi ta diflomasiyya. Kamar yadda aka yi a zagayen da suka gabata, an gudanar da wannan zagaye ba na kai tsaye ba karkashin shiga tsakanin kasar Oman.
An gudanar da zagaye na farko na tattaunawa ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka a Muscat a ranar Juma’a da ta gabata, inda tawagogin Iran da Amurka suka yi musayar ra’ayoyi,