babban mai kula da maslahar iran a kasar masar ya fadi cewa Tehran da Cairo sun yanke shawarar musayar jakadu tsakaninsu, kuma ya bayyana dangantakar dake tsakaninsu ta shiga wani mataki babba da kuma kara zurfafa huldar diflomasiya da kara hadin guiwa kan batutuwan yankin
mojtaba ferdausipour ya fadi a wata hira da yayi da gidan talabijin na Aljazeera cewa wannan mataki na musayar jakadu an yanke shawara akansa yadda ya kamata, kuma sanya ni a matakin jakadu ya tabbatar da wannan shawarwari,
yace dangantaka tsakanin iran da masar ta kara zurfi da inganci fiye da wanda ke tsakaninta da wasu kasashe, a shekarun baya bayan nan shuwagabannin kasashen sun dauki kwararan matakai na kara karfafa dangantaka.
iran ta ce bata da wata damuwa wajen samarwa da kasar masar man da take bukata kuma tana cikin shirin idan aka samu bukatar haka a hukumance daga bangaren Masar, sai dai har yanzu babu wata bukata da alkahira ta gabatar.