Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bukaci Jakadan kasar Jamus a Tehran ya zo ma’aikatar don gabatar da korafin kan matakan da gwamnatin kasar Jamus ta dauka kan JMI a hukumanci.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar ma’aikatar harkokin waje a nan Tehran na cewa Jakada Axel Dittmann ya je ma’aikatar harkokin wajen a nan Tehran bisa gayyatar Alireza Yousufi darakta mai kula da sashen yammacin Turai a ma;aikatar inda ya gabatar masa da korafi mai tsanani kan yadda gwamnatin kasar Jamus a fili ta bayyana goyon bayanta ga tashe-tashen hankulan da suka shirya don kifar da gwamnatin JMI a farkin wajen Jeneru na wannan shekarar.
Yousufi ya kara da cewa matakin da gwamnatin Jamus ta dauka ya sabawa dokokin kasa da kasa dangane da kasashe masu zaman kansu.
Kafin haka wazirin kasar Jamusa Friedrich Merz a kwanakin baya ya bayyana cewa kwanakin gwamnatin JMI a lissafe suke, wanda yake nuna irin hannun da gwamnatin kasar Jamus take da shi a tashe tashen hankulan da suka faru a kasar a farkon wannan shekarar.
Kasar Jamus tana tafiya tare da Amurka a dai dai lokacinda donal Trump yake barazanar kai kaiwa kasar Iran hare-hare wadanda zasu kawo karshen JMI.