Hizbullah Ta Kasar Lebanon Ta Ce Bata Son Yaki Amma Idan An Tilasta Mata A Shirye Take

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Naeem Qasim ya ja kunnen HKI kan hare-hare da take kaiwa kan kudancin kasar Lebanon kusan ko

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Naeem Qasim ya ja kunnen HKI kan hare-hare da take kaiwa kan kudancin kasar Lebanon kusan ko wace rana, a kudancin kasar, wadanda kuma suke lakume rayuwan mutanen yankin.

Ya ce kungiyar sa bata son yaki da HKI ammam halin da ake ciki a kudancin kasar Lebanon na keta hurumin yarjeniyar da aka kulla da HK ba zai dore ba. Don tabbas sai kungiyar ta kawo karshen hakan.

Ya ce a halin yanzu tana bawa gwamnatin kasar Lebanon damar ta aikata abinda ya hau kanta na tabbatar da zaman lafiya a kudancin kasar Lebanon. Sannan ya kara da cewa kungiyar tana kallon yanayin siyasar kasar ta Lebanon don sanin matakan da zata dauka a kan wannan matsalar.

Kamfanin dillancin labaran Iran Press ko IP na kasar Iran ya nakalto babban sakataren kungiyar na Hizbullah Sheikh Naeem Qasim yana fadar haka a jawabin da ya gabatar a kafafen bidiyo a kasar da kuma duniya a jiya Litinin a ranar tunawa da shuwagabannin kungiyar Shahidai wato Tshohon babban sakatarin Kungiyar Shahida Abbas Musawi da babban kwamandan sojojin kungiyar SHahida Imad Moughniyeh sai kuma shahid sheikh Ragib Harba, duk wadanda sojojin HKI suka kai ga shahada a cikin shekarun da ta dauka tana gwagwarmaya da ita.

Dangane da gwamnatin kasar Lebanon kuma Sheikh Qasim kungiyarsa bata tare da mika kai ga bukatun kasashen Amurka da HKI da take yi, don su suna nufin yakar kungiyar hizbullah ne da kuma wargaza kasar Lebanon kanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted