Jaridar Ma’ariv ta HKI ta bada sanarwan cewa bayanan da jami’an tsaron kasar suka gano, kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta tara kan zirga zirgin jiragen ruwa da wasu muhimman kayakin aikin sojen kasar ya firgitar da Jami’an tsaron kasar har kuma ya sa ta gudanar da atisayen soje na baya bayan nan.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar HKI na cewa kungiyar tana da bayanai masu zurfi dangane da asiran harkokin tsaron kasar. Kafin haka jami’an gwamnatin HKI sun bada sanarwan cewa sun gano cewa wani babban jami’an tsaron kasar Amad Amahz yana aiki kud da kud tare da kungiyar Hizbullah kuma bayanan tsaron kasar da dama sun sulale sun shiga kasar.