Binciken da wasu masana suga gudanar sun nuna cewa sojojin HKI suna amfani da makamai masu tsananin zafi wadanda suke kona gawakin falasdinawa a cikin karamin lokaci hatta gawakinsu ba za’a samu ba.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto wani shiri na musamman wanda tashar talabijin ta Al-Jazeera na Larabci ta watsa, dangane da hakan. Labarin ya kara da cewa tun watan Octoban shekara ta 2023 sojojin HKI suka fara amfani da makamai daban daban a kan falasdinawa daga ciki har da makamai masu samar da zafin da ya kai tsakanin ma’aunin celciuos 3000.
Rahoton ya kara da cewa a safiyar ranar 10 ga watan Augustan shekara 2024 Yasmin Mahani ta raste cikin hayaki tana neman danta Sa’adu a cikin makarantar Al-Bain a gaza. Amma sai taga cewa tana taka sauran jini da kuma naman jikin mutum wanda yake kusmus.
Daga karshe ta koma daga inda ta fito ba tare da samun ko gawan danta don yi masa jana’iza ba. Ta ji mijinta yana koka amma daga baya ko gawansa bata gani ba.
Jami’an kiwon lafiya a gaza sun bayyana cewa sun kasa ganowa gawakin falasdinawa kimani 2,842 wadanda suka bace, kuma suna ganin makaman da sojojin HKI ta yi amfani da su a kansu ne suka konasu kurmus bayan sun samarda zafi wanda ya kai ma’aunin zafi celcious 2500-3000 wanda yake gona gawakinsu cikin kebtawar ido.