An zabi kasar Iran a matsayin mataimakin shugaban hukumar bunkasa zamantakewa na MDD. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa a taron hukumar (CsocD) na 64 ne a birnin New York wanda aka gudanar daga 2-10 ga watan Fabrairu na wannan shekara ta 2026 aka gudanar da zaben. Kuma Iran zata ci gaba da rike wannan matsayin na tsawon shekara guda.
Hukumar Csocd dai daya daga cikin hukumomi karkashin babban hukumar ECOSOS ne, kuma aikinta ita ce bada shawara ga hukumar kan al-amuran zamantakewa a duniya. Hukumar tana taimakawa MDD kan mafi yawan shirye-shiryenta na ci gaba da zamantakewa a duniya. Wanda kuma yake taimaka wajen samar da ayyukan yi ga mutane a dukkan kasashen duniya da kuma basu rayuwa mai inganci.