Ministan gina tituna da raya birane na kasar Iran ta bayyana cewa juyin juya halin musulunci a kasar Iran ya sami nasara a kasar Iran a shekara ta 1979 ne tare da goyon bayan mutane, sannan har yanzun masana basu kammala bincike don sanin irin karfin tasirin da wannan juyin juya halin yayi a cikin kasar Iran da kuma sauran kasashen duniya a bangaririn siyasa tattalin arziki zamantakewa da sauransu ba.
Malaman Farzaneh Sadegh ta bayyana haka ne a jawabin da ta gabatar a karamin ofishin jakadancin JMI dake birnin Istambul na kasar Turkiya a iya alhamis.
A jiya alhamis ne karamin offishin jakadancin JMI ta gudanar da taro da bikin cika shekaru 47 da nasarar juyin juya halain musulunci a kasar Iran inda ya gayyaci ministan a matsayin babbar bakuwa mai jawabi a taron.