Shugaba Pizishkiyan: Al’ummar Iran Ta Fito Ne Domin Kare Kasar Da Juyin Juya Halin Musulunci

Shugaban kasar Iran wanda ya gabatar da jawabi a wurin gangamin miliyoyin mutanen kasar domin raya rayar 22 ga watan Bahman na cin nasarar juyin

Shugaban kasar Iran wanda ya gabatar da jawabi a wurin gangamin miliyoyin mutanen kasar domin raya rayar 22 ga watan Bahman na cin nasarar juyin musulunci, ya ce; A yau duniya za ta ga yadda al’ummar Iran su ka fito domin kare kasa da kuma juyin juya halinsu.”

Shugaban kasar ta Iran ya kara da cewa; Wannan rana ce daga cikin ranakun Allah, wanda a cikinsa ne mutane su ka kalubalanci girman kai, kuma Amurka da kasashen turai sun gajiya a fada da juyin musulunci.”

Haka nan kuma shugaban kasar ta Iran ya ce; Al’ummar Iran sun yi juyin juya hali ne, domin shimfida adalci, da kuma rayuwa cikin’yanci, kuma domin mu tabbatar da cewa, musulmi za su iya tafiyar da kasashensu.”

Haka nan kuma ya yi Ishara da cewa; hotunan mutanen da aka cika fagagen gangamin da su, su ne wadanda su ka daukaka matsayin Iran, tare da yin kira ga al’ummar kasar da a koyaushe su zama masu karanta tarihin wadannan manyan mutanen.”

Shugaba Fizishkiyan ya kuma ce; shugabannin Iran a shirye suke, su saurari Koken al’ummar kasa, yana mai kara da cewa; Aikinmu shi ne yi wa al’ummar kasa hidima, kuma abinda makiya suke yi shi ne cutar da al’umma.”

Da yake Magana akan alaka da kasashen makwabta, shugaban kasar ta Iran ya ce; Abinda muke kokarin yi shi ne kyautata alakarmu da kasashen makwabta akan ‘yan’uwantaka, domin wannan ce nashiyar jagoran juyin musulunci.”

Haka nan kuma ya yi wa kasashen makwabtan jinjina da su ka rika tuntubarsa domin nuna goyon bayan Iran akan barazanar da Amurka ta rika yi mata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted