Sojojin Sudan sun cimma nasarori masu yawa tare da ‘yantar da birane a Kudancin Kordofan
Dage killacewar da Rundunar Kungiyar Rapid Support Forces ta Dakarun Kai Daukin Gaggawa ta yi wa biranen Sudan ya nuna wani muhimmin sauyi a ayyukan sojin kasar, bayan nasarar da sojojin Sudan suka samu wajen ‘yantar da Dilling da Kadugli a Kudancin Kordofan.
Hare-haren da sojojin Sudan suka kai a Kordofan da Darfur kan ‘yan tawaye sun taimaka wajen dawo da kwanciyar hankali da kuma isowar kayan agaji da na kasuwanci, bayan wani lokaci na karancin abinci mai yawa sakamakon killacewar da ‘yan tawaye suka yi wa biranen Kudancin Kordofan da hauhawar farashi, wanda ya fara raguwa bayan isowar ayarin motocin kasuwanci na farko a Kadugli.