Duniya na ci gaba da tir da Allah wadai da shirin Isra’ila na mamaye gabadayen yammacin kogin Jodan.
Ministocin harkokin waje na kasashen Larabawa da na Musulunci guda takwas, a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, sun yi Allah wadai da ayyukan gwamnatin Isra’ila, da suka hada da ayyukan gina matsugunan Yahudawa da kuma korar Falasdinawa daga gidajensu.
Sun jaddada cewa gwamnatin Sahayoniya ba ta da ikon mallaka a kan yankunan Falasdinawa da aka mamaye.
Kasashen Pakistan, Masar, Jordan, Hadaddiyar Daular Larabawa, Indonesia, Turkiyya, Saudiyya, da Qatar sun yi Allah wadai da kakkausan murya da matakin da Isra’ila ta dauka ba bisa ka’ida ban a tafiyar da harkokin gudanarwa a Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye.
Wannan matakin tamkar wani shiri ne na Isra’ila na korar Falasdinawa daga gidajensu.
Ita ma kungiyar gwagwarmayar Falasیinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da sabbin matakan na mulkin mallaka” da gwamnatin Isra’ila ta amince da su da nufin mamaye Yammacin Kogin Jordan.
Wannan dai na zuwa ne bayan da majalisar ministocin gwamnatin Isra’ila ta amince da matakai daban-daban da aka tsara don hanzarta ayyukan matsugunan Yahudawa a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye da kuma karfafa ikon gwamnatin a yankin.
Waɗannan matakan suna karkashin jagorancin ministocin nan biyu na Isra’ila masu tsatsauran ra’ayi na kin jinin Falasdinawa wato Ministan Kudi Bezalel Smotrich da Ministan Tsaro Israel Katz.
Shi ma Babban Sakataren MDD António Guterres ya nuna matukar damuwa tare da yin Allah wadai da shawarar da Isra’ila ta yanke na fadada matsugunan da kuma fadada ikon gudanarwa a kan Yammacin Kogin na Jordan.
Fadar White House ma ta Amurka ta ce shugaban Trump, baya goyan bayan matakin na gwamnatin Isra’ila