Dr.Ali Larijani Zai Nufi Kasar Oman Domin Tattaunawa Da  Mahukuntanta A Gobe Talata

Kamfanin dillancin labarun “Irna” na Iran ya bayar da labarin cewa; Babban magatakardar majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani zai kai Ziyara

Kamfanin dillancin labarun “Irna” na Iran ya bayar da labarin cewa; Babban magatakardar majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani zai kai Ziyara kasar Oman a gobe Talata tare da wata babbar tawaga da za ta rufa masa baya.

Majiyar ta ce a yayin wannan ziyarar Dr. Ali Larijani zai gana da jami’an kasar Oman domin tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu ta fuskoki mabanbanta. Haka nan kuma za su tattauna halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya da kuma a fagen kasa da kasa.

A makon da ya shude ne dai aka yi tattaunawar bayan fage  a tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci da kuma tawagar Amurka a karkashin Steve Wittkov dangane da batun makamashin Nukiliyar Iran.

Ministan harkokin wajen Iran din Abbas Arakci ya bayyana ganawar da cewa ta yi armashi, kuma ci gabanta yana da alaka ne da matakan da kasashen Iran da Amurka za su dauka.

A can Amurka shugaban kasar, Donald Trump ya ce, tattaunawar ta yi kyau matuka.

An tsayar da cewa dai a cikin mako mai zuwa ne za a ci gaba da tattaunawar ba tare da an tantance inda za a yi ta ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted