Gwamnatin Kasar Habasha ta zargi kasar Eritrea da mamaye yankinta
Kasar Habasha ta zargi maƙwabciyarta Eritrea da “aiwatar da zalunci kai tsaye” da kuma mamaye wasu sassan yankinta, a wani sabon yanayi da ke barazanar ƙara ta’azzara rikici tsakanin ƙasashen biyu da kuma farfaɗo da yaƙi a yankin Afirka.
Wasikar da Ministan Harkokin Wajen Habasha Gideon Timotheos ya rubuta wa takwaransa na Eritrea, Osman Saleh, ta zargi Eritrea kai tsaye da mamaye yankin Habasha a kan iyakar da ke tsakaninsu na tsawon lokaci.
Wasikar, wacce aka rubuta a ranar 7 ga watan Fabrairu, ta bayyana cewa “shigar da sojojin Eritrea cikin yankin Habasha ba wai kawai tsokana ba ne, har ma da kai hari kai tsaye.”
Adis Ababa ta buƙaci a cikin wasiƙarta da a janye sojojin Eritrea nan take da kuma dakatar da duk wani nau’in haɗin gwiwa da ƙungiyoyin masu dauke da makamai.
Ministan Harkokin Wajen Habasha ya yi gargaɗin cewa: Abubuwan da suka faru kwanan nan suna nuna “ƙara ƙaruwar bullar rikici,” yana mai lura da atisayen soja na haɗin gwiwa tsakanin sojojin Eritrea da ƙungiyoyin masu dauke da makamai na Habasha kusa da kan iyakar arewa maso yamma.