Duk wata kasada ta abkawa Iran da yaki zata wargaza yankin baki daya (Janar Mousavi)

Babban Hafsan Sojojin Iran, Manjo Janar Abdolrahim Mousavi, ya yi gargadi cewa duk wata kasada ta aukawa kasar da yaki zata wargaza yankin ne baki

Babban Hafsan Sojojin Iran, Manjo Janar Abdolrahim Mousavi, ya yi gargadi cewa duk wata kasada ta aukawa kasar da yaki zata wargaza yankin ne baki daya.

Ya kuma kara da cewa tabass hakan kuma zai haifar da shan kaye na makiya a hannun Iran.

“Makiyan Iran sun san cewa duk wani gigi ko kasada na yakar Iran da yaki zai fadada rikicin zuwa dukkan yankin.

Janar Mousavi ya yi wannan a zagayowar ranar Rundunar Sojin Sama ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

“A yau, Rundunar Sojin Sama tana cikin shiri mafi girma, tare da cikakken hadin gwiwa da sauran rundunonin, kuma a shirye take ta bayar da martani mai tsauri, cikin sauri, da kuma kwarin gwiwa ga duk wata barazana, daga abokan gaba, ” in ji shi.

“Iran ba za ta taba fara yaki ba, amma ba za ta yi jinkirin kare tsaron kasarta, muhimman muradunta, da kuma cikakken ikonta na yankuna ba,” in ji Babban Hafsan Sojojin kasar, Manjo Janar Abdolrahim Mousavi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted