Iran: Tattaunawa da Amurka ta takaita ne kawai kan batun nukiliya

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ta takaita ne kawai ga batutuwan da suka shafi nukiliya, ba

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ta takaita ne kawai ga batutuwan da suka shafi nukiliya, ba tare da wata tattaunawa kan wasu batutuwa ba.

Da yake magana da kamfanin dillancin labaran IRNA, Araghchi ya jaddada cewa Tehran ta bayyana matsayinta ga Washington a lokacin da aka tuntube ta.

“Batun tattaunawarmu batun nukiliya ne kawai, ba mu  tattauna da Amurka kan wasu batutuwa ba,” in ji shi.

A cewar ministan, Iran ta isar da wannan matsayin ga wakilan Amurka yayin tattaunawar da aka gudanar a Oman.

“Tabbas, tattaunawa kan batutuwan nukiliya da warware muhimman batutuwa ya kamata kan hakan, ta gudana cikin yanayi mai kyau, ba tare da tayar da jijiyoyin wuya ko barazana ba. Duk wata tattaunawa tana nufin cewa ya zama dole a guji barazana da matsin lamba. Mun bayyana hakan a yau,” in ji shi.

Jawabin nasa ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kokari na diflomasiyya da nufin magance takaddamar da aka haifar kan  shirin nukiliya na Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted